151014-Matsayin-kasar-Rasha-da-kasashen-yamma-kan-rikicin-Sham-Sanusi.m4a
|
Shugaba Putin na Rasha ya ce, hare-haren da dakarunsa ke kaiwa kan 'yan ta'adda, zai taimaka wajen samar da yanayin da ya dace ga 'yan siyasar kasar Syria ta yadda za su yi bani-gishiri-in-baka manda.
Kasashen yammacin duniya karkashin jagorancin Amurka na adawa da matakan soja da Rasha ke dauka a Syria. Ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa, sojojinta za su dakatar da shirinsu na horas da kungiyar 'yan adawar kasar Sham, inda za a maye gurbin shirin ta hanyar tallafa musu da makamai domin yakar mayakan kungiyar IS.
Masana a harkar tsaro na ganin cewa, dari-darin da Amurka ke yi game da musayar bayanan sirri game da Syria ba zai kawo wani cikas ga matakan sojan da Rasha ke dauka a Syria ba.
Masu fashin baki na cewa, matakin Amurka da kawayenta kan Syria ba zai rasa nasaba da wata boyayyar manufa kan Syira ba, wanda kuma ya sabawa kokarin hada kan 'yan Syria na kawo karshen rikicin kasar da ya yi sanadiyar dubban rayukan jama'a. (Ibrahim/Sanusi Chen)