151014-dan-Afrika-na-farko-da-ya-samu-lambar-yabo-bako.m4a
|
Garba Innousa, wani ma'aikacin kamfanin yin na'urar canja karfin wutar lantarki mai suna TBEA-Hengyang ya samu wannan lambar yabo, kuma ya kasance dan Afrika na farko da ya samu wannan lambar yabo, gami da samun ganawar firaministan Sin Li Keqiang cikin shekaru 25 da suka gabata.
Yayin da malam Innousa ya tuna da ranar, ya ce, a cikin wadanda suka samu wannan lambar yabo, har ma da akwai wani kwararren kasar waje, ya taba samun lambar yabo ta Nobel. Duk da cewa, wannan lamba ba ta da girma kamar Nobel, amma ya shaida kaunar al'ummar Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.3. Ya yi mugun alfahari da wannan yabo. Ya ce, zai ci gaba da kokari don yada kayayyakin da aka kera a kasar Sin zuwa kasashen Afrika da ma raguwar kasashen duniya.
Innousa Garba da ya fito daga kasar Kamaru, ya samu digiri na uku game da kimiyya da gine-gine a kasar Sin, kuma ya shiga cikin kamfanin a shekarar 2012, ya tashi tsaye don taimakawa kasashen Afrika wajen samun kudin rance daga kasar Sin, don sayen nau'rorin samar da wuta a kasashensu. (Bako)