Ministan kula da harkoki cikin gida na Guinea Mamoudou Cisse ya ba da wata sanarwa ta wani gidan rediyon kasar, inda ya yi Allah wadai da tashe-tashen hankali dake kawo illa game da zaman rayuwar jama'a da zaman lafiyar al'umma kafin babban zaben kasar.
A cikin sanarwar, an ce, ko magoyon bayan gwamnatin ko na 'yan adawa, ya kamata sojoji su bi akidar samar da zaman lafiya sannan su kai zuciya nesa. Sai dai ba a ambaci wurin da arangamar ta faru ba tsakanin 'yan adawan da sojojin.(Bako)