in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron ministocin kiwon lafiyar Sin da Afirka karo na 2
2015-10-08 10:49:00 cri

Bayan tattaunawar da aka yi a yayin taron ministocin kasar Sin da kasashen Afirka kan hadin gwiwar kiwon lafiya karo na 2 da aka gudana daga ranar 4 zuwa ranar 6 ga wata, wakilan da suka halarci taron sun zartas da "sanarwar Cape Town ta taron ministocin Sin da Afirka kan hadin gwiwar kiwon lafiya karo na 2" da "tsare-tsaren aiwatar da sanarwar Cape Town ta taron ministocin Sin da Afirka kan hadin gwiwar kiwon lafiya karo na 2".

Mambar hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma mataimakiyar firayin ministar kasar Sin Liu Yandong ta aika sako domin tayar murnar kirar taron, inda ta bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ana gudanar da hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka yadda ya kamata. A yayin taron shugabanni na musamman na babban taron MDD da aka yi ba da dadewa ba, aka gabatar da sabon nufi cewa, ya kamata a tabbatar da ko wane mutum a duk fadin duniya ya samu damar jin dadin zaman rayuwa da jiki mai lafiya. Taron da aka yi a Cape Town ya dace da sabuwar bukatar jama'ar Sin da Afirka a wannan fanni, kuma ya dace da sabon nufi na ci gaban aikin kiwon lafiya. Saboda haka, kasar Sin za ta yi hadin gwiwa da kasashen Afirka a karkashin taimakon zamantakewar al'ummar kasashen duniya domin kara karfafa hadin gwiwar kiwon lafiya tsakaninsu, ta yadda za a kara kyautata lafiyar jikin jama'ar kasashen yadda ya kamata.

Yayin taron, daraktar hukumar kiwon lafiya da shirin tsara iyalai ta kasar Sin Li Bin ta yi jawabi, inda ta yi nuni da cewa, Sin kasa mai tasowa ce mafi girma a duniya, Afirka nahiya ce mai cike da kasashe masu tasowa, ban da haka kuma, yawan jama'ar Sin da Afirka ya yi yawa, har ya kai kashi 1 bisa 3 daga cikin dukkan jama'ar duniya. Tabbatar da nufin samun dauwamammen ci gaba a kasar Sin da kasashen Afirka na da muhimmanci kwarai ga ci gaban dan Adam da zaman karko da wadata na kasashen duniya. Wannan taro zai sa hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin Sin da Afirka ya shiga wani sabon matsayi.

Li Bin ta ce, nan gaba ya kamata a kara mai da hankali kan aikin tsara tsarin kiwon lafiyar jama'a, saboda hakan zai kara daga matsayin kiwon lafiya na Sin da Afirka daga duk fannoni.

Li Bin ta kara da cewa, Sin za ta yi hadin gwiwa da kasashen Afirka a kan wasu muhimman ayyukan kiwon lafiyar jama'a, misali rigakafi da kuma shawo kan cutar malariya, da lafiyar jikin mata da yara da sauransu, wato za a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin asibitoci da kamfanoni na sassan biyu. A cikin shekaru 3 masu zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta aika likitoci 1500 zuwa ga kasashen Afirka, kuma za ta shirya wasu ayyukan ba da jiyya na gajeren lokaci a kasashen Afirka guda 40.

Ministan kiwon lafiya na kasar Afirka ta Kudu Pakishe Aaron Motsoaledi ya ce, wannan taro ba taro ne na hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin Sin da Afirka kawai ba, har ma shi ne babban danba na ci gaban hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Idan kasashen Afirka suna son sake tsara tsarin kiwon lafiya da zai dace da halin da suke ciki yanzu, to, ya fi kyau su yi hadin gwiwa tare da kasar Sin, saboda Sin da Afirka suna da matsaya guda daya.

Kuma sanarwar Cape Town da aka zartas da ita a yayin taron ta nuna cewa, kasashen da suka halarci taron za su dauki matakai a jere tare domin kara zurfafa hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin Sin da Afirka. Gaba daya ministocin kiwon lafiya da suka halarci taron sun bayyana cewa, sanarwar za ta samar da sabon tsari wajen daidaita matsalolin kiwon lafiya da kasashen Afirka ke fuskanta.

Wakilai kusan 200 da suka zo daga kasashen Afirka sama da 40 da hukumar kiwon lafiyar kasashen duniya da hukumar shirin cutar AIDS ta MDD da hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun halarci taron.

An yi taron karo na farko a birnin Beijing na kasar Sin a watan Agustan shekarar 2013.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China