in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattawan Najeriya za ta fara tantance ministoci a makon gobe
2015-10-07 14:49:02 cri
A ranar Talatan makon gobe ne majalisar dattawan Najeriya za ta fara zaman tantance sunayen mutanen da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar mata a matsayin ministocinsa

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki shi ne ya bayyana hakan a kwaryar majalisar bayan da ya karanta sunayen ministocin a karon farko, makonni biyu tun bayan da aka mikawa majalisar takardar sunayen a hukumance. Matakin da ya kawo karshen rade-raden da jama'a ke yi game da rashin bayyana ministocin na tsawon watanni.

Daga cikin sunayen ministocin da shugaban majalisar dattawan ya karanta, har da tsoffin gwamnoni biyar, tsofon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya,kakakin jam'iyyar APC mai mulki da kuma manajan darektan kamfanin mai na kasar.

A ranar 30 ga watan Satumba ne shugaba Muhammadu Buhari ya mikawa majalisar dattawan kasar kashi na farko na sunayen ministoci 21 daga cikin a kalla sunaye 36 da ake fatan nadawa a wannan mukami domin ta tantance.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China