in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alkawarin da kasar Sin ta yi zai taimaka ga aikin kiyaye zaman lafiya na MDD
2015-10-05 13:57:57 cri
Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya Herve Ladsous ya bayyana cewa, alkawarin da kasar Sin ta yi na kafa wata rundunar kiyaye zaman lafiya mai dakaru 8,000 zai taimaka wajen cike babban gibin da ake fuskanka a ayyukan kiyayen zaman lafiya na MDD.

Mr. Ladsous wanda ya bayyana hakan cikin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya ce, sanarwar da kasar Sin ta bayar na kafa rundunar ko ta kwana wata babbar gudummawa ce da za ta iya cike babban gibin da ake fuskanta tare da taimakawa dakarun da ke aikin kiyaye zaman lafiya sauke nauyin da aka dora musu.

Jami'in na MDD ya bayyana godiyarsa ga alkawarin da kasar Sin ta yi na taimakawa ayyukan kiyayen zaman lafiya na MDD.

A ranar 28 ga watan Satumba ne shugaba Xi jinping na kasar Sin ya sanar da hakan lokacin da ya ke jawabi a taron kolin wanzar da zaman lafiya na MDD da ya gudana a hedkwatar MDD, inda ya ce, kasar Sin za ta jagoranci aikin kafa tawagar 'yan sandan wanzar da zaman lafiya ta dindindin, sannan kuma za ta kafa rundunar kiyaye zaman lafiya ta ko ta kwana mai dakaru 8,000.

Bugu da kari, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta samar da tallafin dala miliyan 100 cikin shekaru 5 ga harkokin sojan kungiyar AU don kawo karshen tashe-tashen hankulan da ke faruwa a nahiyar.

Har ila, a cewar shugaba Xi, kasar ta Sin za ta tura jirgi mai saukar ungulu a karon farko zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya da MDD ke gudanarwa a nahiyar Afirka.

Kasar Sin ta dade tana hada kai tare ba da gudummawa ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, kuma wadannan sabbin matakan da Sin ta dauka sun kara nuna irin gudummawar da ta ke bayar wa ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.

Alkaluman MDD na nuna cewa, kasar Sin ta shafe shekaru 25 tana shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD kuma yanzu haka ta tura sama da dakaru 3,000 da ke gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya, kana ita ce kasar da ta fi tura yawan dakaru daga cikin kasashe biyar masu kujerun din-din-din a kwamitin sulhu na MDD.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China