in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar Murnar cika shekaru 66 da kafuwar sabuwar kasar Sin
2015-10-01 17:56:53 cri

Ranar 1 ga watan Oktoban kowace shekara, rana ce da Sinawa ke murnar ranar da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949.

A wannan rana ce Sinawa karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), suka ayyana nasarar 'yantar da kasar, bayan gwagwarmaya, inda aka shirya gagarumin biki a dandalin Tian'anmen da birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin.

Yayin wannan biki ne shugaban kasar Sin na wancan lokaci Mao Zedong, ya ayyana kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin, inda ya daga tutar kasar ta farko da kansa.

Tun wannan lokaci ne kasar Sin take bunkasa a fannoni daban-daban, har zuwa yanzu da ta kasance kasa ta biyu mai karfin tattalin arziki a duniya.

Saboda muhimmancin wannan rana ne, ya sa gwamnatin kasar Sin ta kebe mako guda cur a matsayin ranakun hutu, inda 'yan kasar Sin ke amfani da wannan lokaci don ziyartar wuraren shakatawa tare da kai ziyara ga 'yan uwa da abokan arziki.

A cikin wadannan shekaru ne kuma kasar Sin ta yi nasarar fitar da mutane fiye da miliyan 600 daga kangin talauci a sassa daban-daban na kasar. Kuma yanzu haka mahukuntan kasar sun bayyana kudurinsu na rage adadin da ya kai miliyan 10 na matalauta a kauyukan kasar tare da bullo da tsarin kawar da talauci, tsarin intanet da hanyoyin kawar da talauci daban daban.

Masana na cewa, duk kasar da ke son ta samu ci gaba a duniya wajibi ne shugabanninta su kasance masu nuna kishin kasa tare da martaba doka da oda, abin da zai sa su ma 'yan kasa su mutunta shugabannin tare da mutunta duk wasu dokoki da aka shimfida. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China