150925-bikin-tsakiyar-yanayin-kaka-lubabatu.m4a
|
Bikin Zhongqiu na daya daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na Sinawa, wanda a kan yi shi a ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya na kasar Sin, wato ya fado a daidai tsakiyar yanayin kaka, shi ya sa ake kiranta bikin Zhongqiu, wato bikin tsakiyar yanayin kaka. A wannan shekara, bikin ya fado ne a daidai ranar 27 ga wata.Don samun karin haske, sai a biyo mu cikin shirin.(Lubabatu)