in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nemi Japan da ta koyi darussa daga tarihi bayan da aka zartas da dokar tsaron kasar Japan a majalisar dattawa ta kasar
2015-09-19 13:20:21 cri
A daren ranar Jumma'a 19 ga watan nan ne aka zartas da dokar tsaron Japan a majalisar dattawan kasar, wadda ke karkashin jagorancin kawancen jam'iyyun siyasa mai mulkin gwamnatin kasar ta Japan.

Ko da yake jam'iyyun siyasar kasar masu adawa sun yi matukar adawa da zartas da wannan doka, a daya hannun, manufar tsaron kai da Japan ke bi yau da kullum, tun bayan yakin duniya na biyu ta samu sauye-sauye daga dukkan fannoni.

Bisa wannan sabuwar doka, yanzu haka kasar Japan za ta iya tura sojojinta zuwa ketare a ko yaushe kamar kuma yadda take so, bisa bukatar da take da ita, ko kuma ta goyi bayan sojojin sauran kasashen duniya.

Game da wannan doka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mr. Hong Lei, ya ce zartas da sabon shirin tsaron kai a majalissar dattawa ta kasar Japan, mataki ne da kasar Japan ba ta taba daukar makamancin sa ba a fannonin aikin soja, da na tsaron kai, tun bayan yakin duniya na biyu. A 'yan shekarun nan, kasar Japan ta hanzarta bunkasa karfinta na soja, kuma ta daidaita manufofinta na aikin soja da na tsaron kai, wannan mataki bai dace da kokarin shimfida zaman lafiya da neman bunkasuwa, da hadin gwiwa da ake bukata a dukkanin duniya ba. Ya ce irin wannan matakin da kasar Japan ta dauka ya riga ya sanyawa sauran kasashen duniya shakku kan ko kasar Japan za ta yi watsi da manufar tsaron kai kawai, da ma batun ci gaba da bin hanyar neman ci gaba cikin lumana.

Mr. Hong Lei ya ce, a hukumce, kasar Sin ta nemi kasar Japan da ta yi koyi da darussa daga tarihi yadda ya kamata, ta kuma saurari ra'ayoyin daidaikun jama'arta, da na sauran kasashen duniya. Kana kamata ya yi ta maida hankali kan ra'ayoyin kasashen dake makwabtaka da ita game da harkokin tsaron kai.

Hong Lei ya ce kasar Sin tana fatan kasar Japan za ta ci gaba da bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana, kuma ta yi taka-tsantsan game da harkokin soja da na tsaron kai, domin bayar da karin gudummawarta wajen tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Asiya.

A 'yan kwanakin nan, dimbin 'yan siyasa da dubun-dubatar jama'a, da wasu kungiyoyin jama'a na kasar Japan sun gudanar da zanga-zanga, a wani mataki na dakatar da zartas da wannan doka a majalissar dattawan kasar ta Japan. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China