in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana yiwa kamfanonin gwamnatin kasar Sin gyaran fuska
2015-09-16 14:22:12 cri

Tun daga shekarar 2013, gyaran fuska ga kamfanonin dake karkashin ikon gwamnatin kasar Sin, na ci gaba da jawo hankalin jama'a, a waccan shekara, an zartas da "kuduri kan wasu muhimman batutuwa game da yadda za a kara zurfafa gyare-gyaren tattalin arziki daga dukkanin fannoni" yayin cikakken taro na 3, na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, inda aka tanaji babbar manufa game da gyaran fuska kan kamfanonin gwamnatin kasar, kuma aka bayyana cewa, za a yi kokarin ganin an cimma burin kafa wani tsarin kamfanoni na zamani, tare kuma da kafa wani tsarin kasuwa mai dacewa, ta yadda za a iya gudanar da kamfanonin gwamnati, ta yadda za su iya yin takara a kasuwanni yadda ya kamata.

Sakamakon kokarin da ake yi a cikin shekaru biyu da suka gabata, kwanan baya, an fidda wani rahoto mai taken "manufar ba da jagoranci ga aikin zurfafa gyaran fuska kan kamfanonin gwamnati." Rahoton ya kunshi babi 8, wadanda ke dauke da manufofi a fannoni 30. A cikin rahoton, an bayyana cewa, za a fadada tsarin gudanar da manufofin gwamnati da za su dace da tsarin tattalin arzikin kasar Sin, tare kuma da biyan bukatun bunkasuwar tattalin arzikin kasuwar gurguzu, a sa'i daya kuma, za a kafa tsarin kamfanonin zamani, da tsarin gudanar da harkokin masana'antu da kadarar gwamnati mai inganci kafin shekarar 2020.

Game da hakan, mataimakin daraktan kwamitin sanya ido da kula da kadarorin gwamanti na majalisar gudanarwar kasar Sin Zhang Xiwu, ya bayyana cewa, "Yin gyaran fuska game da kamfanonin gwamnati zai taimaka a fannoni uku. Na farko, zai taimaka wajen kara yawan darajar kadarar gwamnati. Na biyu zai taimaka wajen kara karfin gogayyar tattalin arzikin kasar, dai na uku, wato hakan zai taimaka wajen kara habaka amfanin kadarorin gwamnati."

Rahoton ya raba kamfanonin gwamnati kashi biyu, wato irin na kasuwanci da kuma na ababen more rayuwar jama'a, kuma za a iya daidaita matsayin su idan yanayi ya sauya. Game da kamfanonin kasuwanci, an fi mai da hankali kan ribar da za su samu, da kuma karfin gogayyarsu ta kasuwa, iri na samar da ababen more rayuwar jama'a kuwa, an fi mai da hankali kan yawan kudin da za a kashe, da kuma ingancin aikin hidimar da za a samar wa jama'ar kasa daga gare su. Ban da haka kuma, za a karbi ra'ayoyin da jama'ar kasa ke bayarwa, yayin da ake gudanar da bincike kan kamfanoni irin na more rayuwar jama'a.

Mataimakin shugaban kungiyar manazarta kan gyare-gyare da ci gaban kamfanonin kasar Sin Zhou Fangsheng, na ganin cewa, ingancin hidima da farashi na kamfanonin gwamnati, na karkashin jagorancin gwamnati kai tsaye, an kuma fi mai da hankali kan amfaninsu na ba da hidima ga jama'a. Zhou ya ce, "Misali, kamfanonin samar da ruwan famfo, da kamfanin bas bas, da na jiragen kasa na karkashin kasa, suna cikin wadannan rukuni, gwamnatin kasa ta kan samar da kudin rangwame gare su, ba zai yiwu ba su daga farashi kamar yadda suke so, gwamnati ce take gudanar da aikin. Amma irin na kasuwanci kuwa kan yi takara bisa tsarin kasuwa."

Don gudanar da tattalin arzikin kasa da na kasuwa yadda ya kamata, kasar Sin za ta kara bunkasa hadadden tsarin tattalin arziki, wato za a hada kamfanonin gwamnati da na masu zaman kansu, wannan batu shi ma ya jawo hankalin jama'a.

Game da takardun hada-hadar kudin da ma'aikatan kamfanoni suke iya saya, rahoton ya yi nuni da cewa, masu aikin nazarin kimiyya da fasaha, da masu aikin gudanar da harkokin kamfanoni, da sauran ma'aikatan da suka fi ba da gudummawa ga ci gaban kamfanonin, a nan gaba suna iya sayen takardun hada-hadar kudin kamfanonin su.

Mataimakin shugaban kungiyar masu nazari kan gyare-gyare da ci gaban kamfanonin kasar Sin Zhou Fangsheng ya ce, "Idan kowa na da damar sayen takardun hada-hadar kamfanoni, hakan ba zai dace ba, saboda hakan ba zai taimakawa bunkasuwar masana'antun ba."

A kasar Sin, jama'ar kasar suna mallakar kamfanonin gwamnati, idan ana son jama'ar kasar su kara samun moriya daga gyaran fuskar da ake yi yanzu haka, zai dace a gabatar da cewa, za a kara mayar da ribar da kamfanonin gwamnati za su samu ga gwamnatin kasa, ta yadda ribar za ta kai kashi 30 bisa dari nan da shekarar 2020, domin kara kyautata zaman rayuwar jama'ar kasa. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China