in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayafai iri daban daban sun kayatar da musulmai mata na lardin Hainan
2015-09-23 08:32:09 cri

Tafiyarmu a wannan karo ita ce birnin Sanya na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin. Akwai kauyuka biyu na kabilar Hui a birnin Sanya, inda ake iya samun musulmai fiye da 8000. Yayin da muke zagayawa a titunan birnin, mun ga yadda kyawawan mayafai masu launuka iri daban daban da musulmai mata ke sanye da su suka zama tamkar wani abin da ya kawatar da wannan karkara.

A birnin Sanya, tsofaffi mata musulmai da ke sayar da wani irin abinci dangin kwakwa da ake kira areca nut a Turance, da 'yan mata 'yan kabilar Hui da ke sayar da lu'ulu'u, kana da musulmai mata da ke aiki a cikin dakunan cin abinci na halal, dukkansu suna sanye da mayafai.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China