Gabannin daukar wannan mataki, kotun kolin kasar ta yanke hukunci cewar, nada Baciro Dja a matsayin Firaiministan kasar da Jose Mario Vaz ya yi ya saba tsarin mulkin kasar.
A bisa tsarin mulkin kasar ta Guinea-Bissau, shugaban jam'iyyar da ta lashe zaben 'yan majalisu shi ne ya dace ya zama Firaiministan kasar. A watan Mayun shekarar bara ne dai, Jose Mario Vaz ya lashe babban zaben kasar bayan da ya yi takarar a jam'iyyar PAIGC kuma ita ce jam'iyya mafi girma a kasar, kuma bayan nasarar tasa ne ya nada shugaban jam'iyyar Domingos Simoes Pereira ya zama Firaiministan kasar. A ranar 12 ga watan Agusta na wannan shekarar, Jose Mario Vaz ya sanar da wargaza gwamnatin dake karkashin jagorancin Domingos Simoes Pereira, a sakamakon rashin jituwa a tsakanin su. Ka zalika a ranar 20 ga watan Augasta ne, Jose Mario Vaz ya nada tsohon ministan harkokin taron ministoci da majalisu Baciro Dja ya zama sabon firaministan kasar, ba tare da la'akari da ra'ayin adawa da jam'iyyar PAIGC ta nuna.(Lami)