in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasashen Sin da Afrika ta kudu sun bukaci karfafa dangantaka tsakanin kasahen biyu
2015-09-03 15:23:09 cri

A ranar talatar nan jami'an gwamnatocin kasahen Sin da Afrika ta kudu sun nuna bukatar dunkulewa da nufin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Wannan kiran dai ya zo ne a yayin da kasashen 2 ke gudanar da wani taro kan sha'anin tattalin arziki dake gudana a birnin Johannesburg na Afrika ta kudun.

Babban jami'i mai lura da al'amurran kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Sin dake Afrika ta kudu Rong Yansong, ya bayyana cewar kasashen 2 na matukar cin moriyar juna sakamakon irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasahen 2 tun shekaru aru aru da suka shude.

Yansong yace dangantakar dake wanzuwa tsakanin kasar Sin da Afrika ta kudu ta fara ne tun a shekarar 2001 bayan rattaba hannun kan yayjejeniyar a tsakanin kasashen 2.

Ya kara da cewar: "An yi kyakykyawan tanadi wanda ya bada dama ga dangantakar dake tsakanin mu ke cigaba da wanzuwa, za mu iya cigaba da hada kan mu ta fuskar gina fasalin cinikayya da sarrafa kayayyaki masu inganci, ina ganin dangantakar dake tsakanin kasahen 2 tana cigaba da bunkasa''.

Yansong yace cikin shekaru 6 da suka gabata an samu bunkasa cinikayyar tsakanin kasahen biyu data kai dalar Amurka biliyan 19 da digo 61, kuma kasar Sin ce babbar kawa ga Afrika ta kudu ta fuskar cinikayya.

Bugu da kari Yangson ya ce kasar sa a shirye take ta tallafawa Afrika ta kudu ta fuskar samar da kwararru a fannonin da suka hada da masana'antu, da harkar noma da hada-hadar kudi.

Ya kara da cewa: "Akwai bangarori da dama da ake da bukatar hadin gwiwa kan su, domin kuwa kasashen 2 na da larduna 18 da suka kulla dangantakar kasuwanci kamar su Shanghai da Durban kamar dai yadda shugabannin kasahen biyu suka ambata".

Rong ya ce taron da ake sa ran gudanarwa a watan Disambar wannan shekara a Afrika ta kudu na dandalin hadin kan Sin da Afrika wato FOCAC a takaice, zai maida hankali ne wajen karfafa dangantakar kasashen 2.

Babban jami'in sashen bunkasa zuba jari da cinikayya na Afrika ta kudu Yunus Hoosen, yace dangantakar dake tsakanin kasahen biyu tana da kyau kuma akwai bukatar cigaba da inganta ta.

Ya kara da cerwa: "A ko da yaushe muna yin nazarin harkar cinikayya da sauran kasashe ne, mun rattaba hannu kan shirin kulla kyakyawar dangantaka da kasar Sin, kuma akwai bukatar mu fadada dangantakar da ke tsakanin mu a fannonin cinikayya, tun a shekarar 2010 kasar Sin itace babbar aminiyar mu ta fuskar huldar kasuwanci wajen sayan kayan mu ko sayar mana da kayayyaki don haka akwai bukatar bunkasa wannan dangantaka".

Hoosen yace akwai bukartar kasar Sin da kasahen Afrika su hada gwiwa ta fuskar zirga zirga ta ruwa da samar da makamashi da harkokin man fetur da iskar gas da lantarki da dai sauransu.

Sannan ya shawarci kamfanonin kasar Sin, da su hada kai da gwamnatocin kasahen Afrikan domin samun damammaki ta hanyar kulla dangantaka da juna.

Kazalika ya nuna bukatar samar da wani tsari da zai taimaka wajen bunkasa kananan kasahe.

Ya kara da cewar: "Ya kamata ku samar da wani tsari na musayar fasaha da bada horo ga kananan kasashe, kuma ku yi aiki da juna ta haka ne za ku samu nasarori a wannan kasa"

A cewar Hoosen kasar Afrika ta kudu ta tanadi wasu damammaki da suka hada da na bada tallafin kudade da wadanda ma ba na kudaden ba ne ga masu sha'awar zuba jari da kulla dangantakar kasuwanci da kasar.

Ya bada misali da kamfanin Hisense na kasar Sin wanda ke Afrika ta kudun a halin yanzu kuma yana aiki da gwamnatin kasar ba tare da fuskantar wata matsala ba.

Janar Manajan kamfanin Shanghai Feilo Acoustice dake Afrika ta kudu Ding Binyan, yace suna kiyaye dokokin kasar Afrika ta kudu wajen gudanar da ayyukan su.

Ya ce kamfanin nasu yana aikin samar da shawarwari ga kwararu da kuma musayar sabbin fasahohin zamani a Afrika ta kudun tun a shekarar 2014.

Taron da aka gudanar a Johannesburg ya samu tallafi daga sashen bunkasa harkokin cinikayya da zuba jari na kasa da kasa dake Afrika ta kudu, da majalisar kasuwanci ta birnin Shanghai na kasar Sin, da dai sauransu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China