in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Darussan yakin duniya na biyu ga rayuwar bil-Adama
2015-09-03 14:55:26 cri

Yakin duniya na biyu shi ne tashin hankali ko yakin soja mafi muni da rayuka suka salwanta a tarihin bil-adama inda aka yi kiyasin cewa, sama da mutane miliyan 60 sun halaka, wato kimanin kashi 3 cikin 100 na yawan al'ummar duniya a shekarar 1940.

Masanan tarihi sun bayyana cewa, alkaluman wadanda suka mutu sanadiyar yakin wanda aka fara a shekarar 1935 zuwa 1945 sun hada da fararen hula sama da miliyan 50 zuwa 55 da mutane miliyan 19 zuwa 28 da suka mutu sanadiyar cututtuka da yunwa da ke da nasaba da yakin, sai kuma sojoji miliyan 21 zuwa 25 ciki har da wadanda suka mutu yayin da ake tsare da su da suka doshi miliyan 5.

Wani binciken ya kuma nuna yadda sojojin Japan suka halaka Sinawa sama da miliyan 20, baya ga wasu mutanen da sojojin Japan din suka halaka a kasashen da ke yankin Asiya.

Kasashen Amurka da Turai sun yi Allah wadai da mamayar da Japan ta yi wa kasar Sin a shekarar 1937, wanda daga bisani suka kakaba wa kasar ta Japan takunkumin mai da na bakin karfe.

A ranar 15 ga watan Agusta na shekarar 1945 kasar Japan ta mika wuya tare da kawo karshen yakin duniya na biyu kana ta amince da yarjejeniyar Postdam.

A ranar 25 ga watan Afrilu na shekarar 1945 ne kasar Sin da kasashen Amurka, da Birtaniya da tsohuwar tarayyar Soviet, suka shirya taron San Francisco, taron da wakilai daga kasashe 50 suka halarta, domin tattaunawa game da tsara kundin tsarin mulkin MDD.

Bayan kawo karshen wannan yaki, yanzu haka kasashen duniya daban daban na shirya bukukuwan cika shekaru 70 da kawo karshen wannan yaki da kuma ra'ayin masu nuna karfi a duniya, a kokarin ganin an shimfida zaman lafiya a duniya.

Masu sharhi na cewa, kamata ya yi kasashen da suka tabka ta'asa a lokacin yakin, su amince da tarihi su kuma nemi gafara ba tare da gindiya wani sharadi ba, ta yadda za su samu karbuwa daga al'ummar duniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China