A jawabinsa yayin bude taron, shugaban kawancen majalisun dokoki na duniya wato IPU Saber Chowdhury, ya ce abin da taron zai bada fifiko a kansa shi ne, batun neman dauwamamen ci gaba. Ya kara da cewar a yanzu haka ana fuskantar kalubale masu yawa wadanda ke dakile cigaba da suka hada da talauci, ricike-rikice, sauyin yanayi, afkuwar bala'o'i da dai sauransu. A don haka shugaban ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai don neman makoma mai kyau.
Ana sa ran kammala babban taron ne a ranar 2 ga watan Satumba, kuma taron ya samu halartar shugabannin majalisun dokoki na kasashe 140, ciki har da shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang. (Bilkisu)