in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta yi wa wasu fursunoni ahuwa yayin bikin ranar 3 ga watan Satumba
2015-08-30 13:15:16 cri
Mahukuntan kasar Sin sun bayyana kudurinsu na yi wa dubban tsoffin fursunonin yaki ahuwa, a yayin bikin cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu da kasar za ta shirya a ranar 3 ga watan Satumba.

Dokar yin ahuwar wadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanyawa hannu a jiya ta zo ne bayan shekaru 40 da yiwa wasu mutanen da suka aikata laifukan yaki ahuwa a shekarar 1975 da kuma shekaru 56 bayan da aka yiwa wasu mutanen ahuwa a karon farko a shekarar 1959.

Daga cikin wadanda za a yiwa ahuwar, sun hada da wadanda ba su kasance barazana ga al'umma ba da ake yanke wa hukunci kafin ranar 1 ga watan Janairu, shekarar 2015.

Na farko su ne wadanda suka shiga yakin kin harin mayakan Japan da yakin basasa da mayakan Koumintang. Na biyu mutanen da suka shiga yakin kare 'yanci, yankuna da tsaron kasar bayan shekarar 1949, amma ban da wadanda aka samu da aikata munanan laifuffuka, ciki har da almobazzaranci da dukiyar jama'a, karbar cin hanci, ayyukan ta'addanci.

Na uku su ne masu laifin da shekarunsu na haihuwa ya haura 75, da wadanda ke fama da wata nakasar da ba za su iya kula da kansu ba. Kana na hudu kuma na karshe cikin wadannan rukunoni, su ne wadanda suka aikata laifuffuka a lokacin da suke kasa da shekaru 18 kana aka yanke musu hukuncin shekaru 3 a gidan yari ko sauransu kasa da shekara guda su kammala wa'adin daurin gidan yarin da aka yanke musu, amma ban da wadanda suka aikata kisan kai, fyade, ayyukan ta'addanci ko laifuffukan da suka shafi ta'ammali da miyagun kwayoyi.

A ranar Asabar ne masu kula da harkokin doka suka amince da matakan yin ahuwar, bayan da kwamitin majalisar wakilan jama'a ya nazarci daftarin kudurin a yayin taron da ya saba gudanarwa sau biyu a kowane wata. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China