150828-Matukin-farko-na-jirgin-kasa-mai-saurin-tafiya-na-jihar-Xinjiang.m4a
|
A shekarun baya, kasar Sin na kokarin raya jiragen kasa masu saurin tafiya, yanzu Sinawa suna iya tafiya zuwa yankunan kasar masu nisa cikin gajeren lokaci, yanzu, hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya sun hada manya ko matsakaitan birane da dama na kasar Sin. Yanzu haka, an shimfida hanyar jirgin kasa mai saurin tafiya zuwa jihar Xinjiang, inda Adil Turdi ya zama matuki na farko na jirgin kasa mai saurin tafiya na jihar Xinjiang.