in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba ta shirya faretin soji domin wata kasa ta musmaman ba, in ji ma'aikatar tsaron kasar
2015-08-28 11:22:37 cri

A yayin taron manema labaran da ma'aikatar tsaron kasar Sin ta kira, batun faretin murnar tunawa da cika shekaru 70 da samun nasara kan mayakan Japan da kuma yaki da masu ra'ayin nuna karfin tuwo a duniya da za a yi a ranar 3 ga wata mai zuwa su ne suka fi jawo hankalin kafofin watsa labarai na cikin gida da na kasashen waje. Bayanai na nuna cewa, ya zuwa yanzu, an tabbatar da cewa, kasashe 49 da kungiyoyin kasa da kasa 10 ne za su halarci bikin faretin soji bisa gayayyar da aka yi musu. Game da tambayar da aka gabarar game da ko kasar Sin tana son nuna karfin sojinta ne ga kasar Japan ta hanyar faretin sojan, kakakin ma'aikatar Yang Yujun ya bayyana cewa, "Faretin sojin da za a yi a ranar 3 ga watan Satumba wani bangare ne daga cikin abubuwan da aka tsara na murnar tunawa da cika shekaru 70 da samun nasara kan mayakan Japan da kuma yaki da masu ra'ayin nuna karfin tuwo a duniya, kuma makasudin sa shi ne tunatar da jama'a cewa, kada su manta da tarihi, da wadanda suka sadaukar da rayukansu a kokarin kiyaye zaman lafiya, tare kuma da tunatar da jama'a cewa, ya kamata su darajanta zaman lafiya yayin da suke kokarin samun makoma mai haske. Kasar Sin ba ta shirya faretin sojin domin wata kasa ta musamman ba, balle ma domin jama'ar kasar Japan ba, a sa'i daya kuma ba shi ba alaka ko kadan da huldar dake tsakanin Sin da Japan."

Yang Yujun ya fayyace cewa, rundunar sojojin kasar Rasha za ta halarci faretin sojin a matsayin rundunar da za ta yi maci na karshe.

Game da kalaman da aka fada a kan yanar gizo wai tankokin yakin sojojin kasar Sin suna kutsa kai zuwa iyakokin kasashen Sin da Korea ta Arewa, Yang Yujjn ya musunta wadannan kalamai, ya ce, "Rahotannin da aka watsa a kan yanar gizo ba gaskiya ba ne, karya ce tsagwaronta, bai kamata jama'a ma su kalle su, Yanzu, halin da ake ciki a iyakokin kasashen Sin da Korea ta Arewa yana da kyau kamar yadda ya kamata, sojojin kasar Sin da ke iyakokin suna samun horo kamar yadda suke bukata."

Yayin taron, Yang Yujun shi ma ya yi bayani kan ci gaban da aka samu kan ka'idar haduwar jiragen sama ba zato cikin sararin samaniya tsakanin Sin da Amurka, ya ce, a watan Nuwanban shekarar da ta gabata, ministocin tsaron kasashen Sin da Amurka suka rattaba hannu kan wata takardar da ta shafi tsari biyu na fahimtar juna, inda suka bayyana cewa, za su iya kara wasu abubuwa a cikin takardar ta hanyar yin tattaunawa. Tun a farkon shekarar bana, bangarori biyu wato Sin da Amurka suka fara yin shawarwari kan batutuwa biyu da suka hada da "ka'idar daidaita hadarin karon jiragen sama a sararin samaniya" da "sanarwar matsalar da ta shafi harkokin soji", kuma sun samu sakamako mai yakini.

Ban da haka, Yang Yujun ya ce, an kara wuraren ganawa tsakanin iyakokin Sin da Indiya har zuwa biyar, an yi hakan ne da nufin magance aukuwar wasu kura-kurai. Yang Yujun ya ce, "Bisa ra'ayi daya da shugabannin kasashen Sin da Indiya suka cimma da yarjejeniyar hadin gwiwa game da iyakokin kasashen biyu da aka daddale, bangarorin biyu wato Sin da Indya za su kafa wuraren ganawa a iyakokinsu, yanzu ana gudanar da aikin yadda ya kamata, kuma ya zuwa yanzu an kara kafa wurare daga 3 zuwa 5, matakin da zai taimaka wajen kara cudanya tsakanin sojojin kasashen biyu." (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China