in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bakin haure 3573 suka hallaka kan bahar maliya cikin shekara 1
2015-08-26 10:00:28 cri

Kungiyar kula da harkokin shige da fice ta duniya IOM ta bayyana cewa, mutane 3,573 ne suka hallaka a lokacin da suke kokarin tsallaka shiga kasashen Italiya, Girka da kuma Spaniya tun daga watan Agustan bara.

Alkalumma na nuna a kalla duk rana mutane 10 kan rasa rayukansu a cikin shekara 1, abin dake nuna yawan masu neman tsallakawa zuwa kasashen Turai yana ci gaba da karuwa da kusan 267,121 masu shiga ta jirgin ruwa da aka samu rahotonsu a wannan shekarar.

Kungiyar ta nuna cewa, kasar Girka kadai ta samu adadin 157,228 da suka shigo ya zuwa yanzu wadda ta zama inda 'yan gudun hijira dake tserewa tashin hankalin kasashen Afganistan, Syria da Iraqi ke saurin shigewa a duk kasashen da ake zuwa.

Italiya kuma tana da mafi girma a yawan wadanda suka shiga kasar a wannan shekara da kusan 107,633 da suka fita daga kasashen Eritrea, Nigeria, Somaliya, Sudan da Syria da suke isa bakin ruwa, sauran kasashen kamar Spaniya na da 2,166, sai Malta guda 94 wadanda idan aka kara ake samun adadin mutanen da ke shiga Turai. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China