in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada sabon Firaiminista a Guinea-Bissau
2015-08-21 11:01:08 cri

Shugaban kasar Guinea-Bissau Jose Mario Vaz ya rattaba hannu inda ya amince da nadin tsohon ministan kula da majalisun dokokin kasar Baciro Dja a matsayin sabon Firaiministan, wanda ya maye gurbin Domingos Simoes Pereira wanda aka sallame shi daga mukaminsa.

Shugaba Vaz ya ce, nadin sabon firaministan ya biyo bayan shawarwarin da jam'iyyu daban daban a majalisar dokokin kasar suka gudanar ne.
Sai dai har yanzu ba a sani ba ko jam'iyya PAIGC mafi girma cikin majalisar dokokin kasar ta amince da wannan nadin. Vaz da Pereira sun kasance 'yan jam'iyyar PAIGC, kuma Pereira shi ne shugaban jam'iyyar.

A ranar 12 ga wata, Vaz ya sanar da rushe gwamnatin kasar dake karkashin shugabancin Pereira, abun da ya kawo zanga-zangar sauran jam'iyyu da al'umma a kasar. Daga bisani, jam'iyyar PAIGC ta bukaci Vaz da ya sake nada Pereira don ya zama firaministan kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China