150819-Shugaban-Najeriya-ya-umarci-dakarun-kasar-da-su-kawar-da-Boko-Haram-cikin-watanni-uku-Sanusi.m4a
|
Shugaba Buhari ya ce, lokaci ya yi da za a kawo karshen kungiyar Boko Haram wadda ta hallaka dubban mutane a cikin fiye da shekaru shida. Ya ce, dole ne manyan hafsoshin su zage damtse, kuma su ci gaba da aiki da sauran masu ruwa da tsaki domin kawo karshen masu tayar da kayar baya.
Bugu da kari, ya ja hankalinsu kan su mayar da hankali wajen kare fararen hula da kuma mutunta hakkin abokan hammaya a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
Da yake jawabi a madadin sauran manyan hafsoshin uku da shugaba Buharin ya rantsar janar Abayomi Gabriel Olonisakin ya ce za su bi umarnin da shugaba ya bayar na ganin an kawar da kungiyar Boko Haram cikin watanni uku
Manyan hafsohin sojin da shugaban ya nada sun hada da Major-General Abayomi Gabriel Olonishakin da Major-General T.Y. Buratai da Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas da kuma Air Vice Marshal Sadique Abubakar.
Tun lokacin da aka rantsar da Buhari a matsayin shugaban Nigeria a karshen watan Mayun shekarar 2015, kungiyar Boko Haram ta zarfafa hare-haren da take kaiwa inda ya zuwa yanzu ta hallaka mutane kusan 900.
A karshen watan Yuli ne rundunar hadin gwiwa kan yaki da Boko Haram mai dakaru 8,700 da ta kunshi sojoji daga kasashen Nigeria da Niger da Kamaru da Chadi da kuma jamhuriyar Benin ta soma aiki.
Sai dai 'yan kwanaki da umarnin da shugaba Buhari na Najeriya ya bayar, sai shugaban Chadi ya fito yana bayyana cewa, kungiyar ta Boko Haram ta nada sabon shugaban da ya maye gurbin Abubakar Shekau, amma daga bisani kuma sai Shekau din ya sake bayyana cikin wani faifan murya mai tsawo mintuna 8 cikin harshen Hausa yana karyata duk wani ikirarin da sojojin Najeriya suka yi cewa, sun kashe jagoran kungiyar.
Masu sharhi na ganin cewa, matakin kungiyar ta fitar da sabon faifan muryar, ba zai sanyaya gwiwar dakarun dake kokarin ganin bayan mayakan na Boko Haram ba. (Ibrahim/Sanusi Chen)