150814-mu-shakata-da-wakoki-masu-dogon-kari-na-Mongoliya-lubabatu.m4a
|
Wakoki masu dogon kari na al'ummar Mongoliya wakoki ne na gargajiya, wadanda aka sanya su a cikin jerin al'adun gargajiya na baka da ba na kayayyaki ba na duniya na kungiyar kula da ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD, wato UNESCO. Bisa tarihi, makiyaya dake arewacin kasar Sin ne suka kirkiri wadannan wakoki, cikin jerin ayyukan su na raya sana'ar kiwon dabbobi, su kan rera wadannan wakoki yayin da suka fita kiwo da dabbobin su, da kuma lokutan bukukuwan al'adu.
Sannu a hankali kuma wadannan wakoki suka fara bin tsari na kabilun yankin na Mongolia, masu cike da amo na musamman da kuma dogon kari. Amon wadannan wakoki mai tsawo na da taushi da tsayi, ana jan sa sosai tare da kayatar da rera su. Wadannan wakoki na Mongolia masu tsayin kari na da tsari na daban, wanda ya kebanci al'adun makiyaya da kuma yankunan da suke da zama. Suna kuma kunshe da madubin tarihi, da tatsuniyoyi, da tarbiya, da ilimin Falsafa da al'adun gargajiya, hade da yaren musamman na al'ummar Mongoliya.
A biyo mu cikin shirin, domin samun karin haske a kan salon wakar tare da shakata da wasu wakokin. (Lubabatu)