Kwanan baya, an yi taron kara-wa-juna-sani na kasashe masu tasowa game da kare al'adu, a yayin taron, wakilinmu Bako ya samu damar a yi hira da Madam Ogohi, direktar kwamitin kula da al'adu da abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni, ta ce, ya kamata kasar Nijeriya ta koyi fasahohin da Sin ta samu wajen kare al'adu da kiyaye abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni.(Bako)