150812-Kasar-Sin-ta-zama-kasa-ta-farko-a-duniya-da-za-ta-shirya-wasannin-IOC-na-zafi-da-na-sanyi-Sanusi.m4a
|
Ko da yake, birnin Alma-Ata na kasar Khazakstan bai samu wannan dama ba, kafofin yada labaru daban-daban na kasar sun darajanta ayyukan da birnin Beijing ya yi, kuma sun amince da cewa, birnin Beijing zai samu nasarar shirya wannan gasa saboda ganin nasarar da ya samu a shekarar 2008.
A cewar shugaba Xi Jinping na kasar Sin, bisa burin da ake da shi na shirya gagarumar gasa mai kayatarwa, wadda za ta dace da burin al'ummar Sinawa biliyan 1.3, gwamnati za ta cika alkawuranta, za kuma a cimma babbar nasarar da ake fata da hadin kan dukkanin al'umma, da goyon bayan kasashe, da shi kansa kwamitin na IOC, ta yadda hakan zai zamo dama ta yada manufar gasar wasannin Olympics a duniya.
Masu fashin baki na ganin cewa, bayanan da kasar Sin ta gabatar na neman daukar bakuncin wannan gasa, manufofi ne da al'ummun yankunan za su dade suna cin gajiyarsu a bangarorin tattalin arziki, sufuri, cinikayya da makamantansu. Yanzu haka, kasar Sin ta kasance kasa ta farko a duniya da ta samu damar shirya gasar wasannin Olympics na lokutan zafi da kuma sanyi a tarihin kwamitin na IOC na sama da shekaru 100. (Ibrahim/Sanusi Chen)