150804-ya-kamata-nijeriya-su-ci-gajiya-daga-dabarun-sin.m4a
|
Kwanan baya, an shirya taron kara-wa-juna-sani na kasa da kasa na masu nazarin kasar Sin a nan birnin Beijing, Shehu malami Abdul da ya fito daga jami'ar Abuja shi ma ya halarci taron, yayin da wakilinmu Bako ke zantawa da shi, ya bayyana cewa, tsarin raya kasar Sin a fannoni 4, wato a raya zaman wadata, da karfafa gyare-gyare, da gudanar da harkokin kasa bisa doka, da yaki da cin hanci da rashawa, kana manufar diplomasiyya da Sin ke gudanarwa na dora muhimmanci sosai game da kasashe makwabtaka sun yi daidai da manufar cikin gida da ta diplomasiyya da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya gabatar, ya ce, ya kamata kasashe biyu su inganta hadin gwiwa tsakanin manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu, don tsara alkiblar raya makomar dangantakar kasashen biyu.(Bako)