in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
M.D.D. ta yi Allah-wadai da harin ta'addanci da aka kai a wani otel da ke kasar Somaliya
2015-07-28 14:38:05 cri

A ranar Lahadi ne, aka kai wani harin bam na kunar bakin wake da aka dasa cikin wata mota a wani otel mai suna Jazeera da ke birnin Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 15, tare da jikkata wasu da dama. Ma'aikatar kula da harkokin wajen Sin ta bayyana cewa, harin ya halaka wani jami'in tsaro dake aiki a ofishin jadakancinta da ke kasar Somaliya, kana wasu ma'aikatu 3 sun ji rauni. Wani jami'in lekan asiri na kasar Somaliya ya bayyana cewa, ana tuhumar wani Bajamushe dan asalin kasar Somaliya da kai wannan harin ta'addanci.

A jiya Litinin ne kuma, zaunannen wakilin Sin da ke M.D.D. Liu Jieyi ya ce, kasar Sin ta girgiza matuka tare da yin Allah-wadai da harin ta'addanci da aka kai. A wannan rana kuma, kwamitin sulhu na M.D.D. da babban magatakardan M.D.D. Ban Ki-Moon sun ba da wata sanarwa, inda suka yi tofin Allah-tsine game da lamarin. Kwamintin sulhu na M.D.D. ya sake nanata kudurinsa na yaki da duk wani irin nau'i na ta'addanci bisa kundin tsarin mulki na M.D.D, a sa'i daya kuma, ya sake jaddada yarjeniniyar raya dangantakar kasa da kasa ta Vienna, don ba da tabbaci ga tsaron lafiyar jami'an diplomasiyya a kasashen waje.

Rahotanni na cewa, bayan aukuwar lamarin, kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya mai alaka da kungiyar Al-Qaeda ta sanar da daukar alhakin kai harin, yayin da kawancen sojojin kungiyar AU ke ci gaba da yaki da kungiyar ta Al-shabaab, kungiyar da ta kashe fararen hula sama da 10 a kasar Habasha a matsayin ramuwar gayya.

Bayanai sun bayyana cewa, akwai ofisoshin jakadancin kasashen yammacin duniya a otel din, kuma su kan yi hadin gwiwa tare da kungiyar AU don yaki da kungiyar Al-shabab. Amma, bisa labarin da wakilinmu ya samu, an ce, babu ofisoshin jakadancin kasashen yammacin duniya a cikin otel din, koda ya ke ofishin jakadancin Sin da ke kasar yana amfani da hawa na 5 da na 6 dake otel din, jami'an diplomasiyya na kasashen Qatar da Masar suna gudanar da aikinsu a wajen, kuma yawancin wadanda ke zaune a cikin otel din, manyan jami'an gwamnatin kasar Somaliya ne da 'yan kasashen waje.

Otel din Jazeera mai nisan kilomita 1 zuwa 2 daga babban filin jiragen saman Mogadishu ya shahara sosai a kasar Somaliya, shi ya sa ake tabbatar da tsaro a wajen, kuma akwai sojojin da ke sintiri a kofofin shiga otel din,baya ga ma'aikatan da ke aikin gadi a ciki da wajen otel din, haka zalika baki kan yi hayar motoci masu sulke daga cikin otel din. Sakamakon haka, bayan harin kunar bakin waken da aka kai otel din ranar Lahadi, abun da ba kowa mamaki, kuma wannan shi ne karo na 3 da kungiyar Al-shabaab ta kai harin kan otel din, koda yake wannan ya kasance hari mafi muni da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 8 da suka gabata.

Abun lura a nan, shi ne, an kai hari ne a daidai lokacin da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kammala ziyara a kasar Kenya da ke makwabtaka da Somaliya, kuma yanzu, yana ziyara a kasar Habasha, a daidai lokacin ne kuma, kungiyar Al-shabaab ta kai hari kan otel Jazeera mai matukar tsaro, don janyo hankulan kasashen duniya. Ganin yadda wannan hari ya kama da ragowar hare-haren da aka kai a baya, kuma ba wai wani hari ne da aka kai kan Basine kawai ba, amma harin na yanzu, ya rutsa da ofishin jakadancin Sin da ke kasar Somaliya tare da jikkata wasu

Wani jami'in leken asiri da ba ya son a ambaci sunansa ya ce, ana tuhumar wani Bajamushe dan asalin kasar Somaliya da hannu a wannan harin da aka kai, ya zuwa yanzu, ana gudanar da binciken lamarin, kuma wasu kwararrun kasashen waje su ma suna bincike a wurin.

Tun lokacin da yakin basasa ya barke a kasar Somaliya a shekarar 1991, kasar ta shiga cikin rudani, lamarin da ya kara baiwa kungiyar Al-Shabaab damar fara aika-aikar ta'addanci, a shekarar 2012, an samu ci gaba cikin yunkurin samar da zaman lafiya a kasar, har aka kafa gwamnati da majalisar dokokin kasar a hukunce, kuma yanayin tsaro da ake ciki a kasar ya dan inganta. A bisa taimakon rundunar tsaro ta kungiyar AU, an samu nasarar fatattakar mayakan kungiyar Al-Shabaab daga manyan biranen kasar, amma, har yanzu, ana fuskantar barazanar ta'addanci a kasar. A farkon watan Satumbar bara ne, aka harbe jagoran kungiyar Ahmed Abdi Godane har lahira a harin da sojojin Amurka suka kai ta sama, kuma wasu kafofin yada labaru sun bayyana cewa, mutuwar Godane za ta kawo wa kungiyar koma baya, har ma zai kawo rarrabuwar kawuna, amma ba da dadewa ba, kungiyar ta sake nada sabon jagora, har ma ta fara kai hare-haren ta'addanci a kasashen Somaliya da Kenya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China