in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata ko wane mutumin Ghana ya tashi tsaye don gina kyakkyawar Ghana
2015-07-29 09:00:25 cri

Kwanan baya, an yi taron bita game da warware batun sauyin yanayi da raya aikin gona na kasashe masu tasowa a nan birnin Beijing, inda wakilinmu Bako ya yi hira da wasu jami'ai daga kasar Ghana a yayin taron.


Mubarak Saliffou, dan kasar Ghana da ya fito daga hukumar deba yanayi ta kasar Ghana, ya gaya wa wakilinmu cewa, bayan da ya halarci taron, yana ganin cewa, ya kamata a kara kokari wajen deba yanayi don warware batun sauyin yanayi da ya shafi Ghana, kuma yana mai cewa, a shekarun baya, yayin da aka samu bala'in ambaliyar ruwa ko wasu bala'u, jama'a su kan korafe-korafe game da ayyukansu, amma yana ganin cewa, ya kamata jama'a su yi hakuri, sabo da ana iya hasashe yanayi cikin awoyi 3 masu zuwa dari bisa dari, amma ba zai iya hasashen yanayi cikin kwanaki 2 ko 3 masu zuwa dari bisa dari ba, kuma yana fata bayan da ya koma gida, zai yi amfani da abubuwan da ya koyo a kasar Sin don kyautata ayyukansa.

Yayin da Adamu Moustapha yana mai cewa, ya kamata ko wane dan kasar Ghana ya yi waswasi, mene ne ya kawo batun sauyin yanayi, kuma shugaban kasar Ghana Alhaji. John Dramani Mahama ya gabatar da burin gina kyakkyawar Ghana, ya kamata ko wane mutum ya yi kokari don ba da gudummawa ga Ghana.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China