150729-Ziyarar-da-shugaban-Najeriya-ya-kai-Amurka-Sanusi.m4a
|
Shugabannin biyu sun tattauna kan muhimmancin hada kai ta fuskar tsaro, musamman yakin da ake yi da mayakan Boko Haram, wanda shugaba Obama ya ce, kungiyar tana kawo koma baya ga kasar ta Najeriya.
Yayin ganawar shugaba Muhammadu Buhari ya mika godiya ga gwamnatin Amurka kan yadda aka samu nasarar gudanar da zabuka a Najeriya.
Bugu da kari, shugaba Buhari ya sha alwashin kwato biliyoyin dalolin da aka sace daga kasar tare da taimakon da Amurka ta yi alkawarin bayarwa, inganta tattalin arzikin kasar da samar da ayyukan yi ga matasa.
A nasa jawabin shugaba Obama na Amurka ya ce, ya gamsu da alkiblar shugabancin Muhammadu Buhari, kuma Amurka za ta hada gwiwa da Najeriya wajen ganin an murkushe 'yan kungiyar Boko Haram da matsalar cin hanci da rashawa da ta yi wa kasar dabaibayi.
Masu fashin baki na cewa, saboda irin muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa wajen ci gaban duniya hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a nahiyar Afirka baki daya.
Bugu da kari ana ganin wannan ziyara za ta kara daukaka martabar Najeriya a idanun duniya, sannan ta kawo karshen zaman doya-da-manja da ake yi tsakanin Amurka da Najeriya sakamakon zargin take hakkin bil adama da Amurka ke yi wa sojin Najeriya. (Ibrahim/Sanusi Chen)