in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NASA ta ce ana gano wata duniya mai kusanci da duniyar bil'adama
2015-07-24 12:51:00 cri

Masana a fannin kimiyya a hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka ko NASA a takaice, sun ce, sun gano wata duniya mai girman gaske wadda aka yiwa lakabi da Kepler-452b.

Masanan sun ce, wannan duniya na kusa da duniyar bil'adama, kuma daya ce daga cikin sauran duniyoyi da dama da aka gano, wadda ke a kewayen sararin sama da ake zaton akwai rayuwa.

Hukumar NASA ta ce, ya zuwa yanzu babu tabbacin ko wannan duniya na kunshe ne da duwatsu ko kuma ruwa, ko da yake akwai hasashen dake nuna cewa, mai yiwuwa ne tana cike ne da duwatsu.

Wannan dai sakamako na zuwa ne gabar da ake cika shekaru 20 da gano wasu duniyoyin na daban dake kan falaki na rana, wadanda masana ke ganin mai yiwuwa a iya rayuwa a cikin su.

John Grunsfeld, masani a hukumar ta NASA, ya ce, wannan mataki na nuni da yiyuwar samun wata duniya da ita da duniyar bil'adama kan iya zama tamkar tagwaye.

A baya dai akwai wasu duniyoyin 12 da aka nazarta, wadanda ba su kai duniyar bil'adama girma ba, wadanda kuma ke kan falakin da ake zaton ana iya rayuwa cikin sa. Sai dai Kepler 452b, wadda ke da nisan tafiyar haske 1,400 daga duniyar mu, ita ce ta farko da masanan ke ganin ta cika sharuddai na musamman na rayuwa.

Kepler-452b dai ta dara duniyar bil'adama girma da kaso kusan 60 bisa dari. Ta kuma zamo ciko na adadin duniyoyi 1,030 da masana suka gano. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China