in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barack Obama zai ziyarci kasashen Kenya da Habasha
2015-07-23 09:43:22 cri

Mashawarciyar shugaban kasar Amurka a fannin tsaro Susan Rice, ta ce shugaba Barack Obama zai gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki 4 a kasashen Kenya da Habasha dake yankin gabashin Afrika.

Rice ta fadi hakan ne , yayin wani taron manema labaru a jiya Laraba a fadar White House. Ta ce shugaba Obama zai zama shugaban Amurka mai ci na farko da zai ziyarci wadannan kasashe 2.

A kasar Kenya, Obama zai yi shawarwari da shugabannin kasar, tare da halartar taron koli na masu masana'antun kasashen duniya, yayin da a Habasha kuma zai ziyarci hedkwatar kungiyar AU.

Rice ta ce, sabo da karancin lokaci, da wasu sauran dalilai na daban, Obama ba zai ziyarci garin Kogelo wanda shi ne mahaifar sa a kasar Kenya ba. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China