150722-Muhimmancin-yarjejeniyar-nukiliyar-Iran-ga-tsaron-duniya-Sanusi.m4a
|
Wannan yarjejeniyar mai cike da tarihi kusan ta soma aiki bayan da kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri kan batuna. Cimma wannan yarjejeniya ya samu yabo sosai daga kasashen duniya, amma a sa'i daya kasar Isra'ila ta nuna rashin jin dadinta da cimma wannan yarjejeniya da ta kira babban kuskure da aka yi a tarihi.
A jawabin da ya gabatar bayan cimma yarjejeniyar, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa, muddin aka zartas da yarjejeniyar yadda ya kamata, to za a kawar da rashin amincewa tsakanin kasarsa da kasashe yammacin duniya.
Shi ma babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, cimma wannan yarjejeniyar na bukatar a gudanar da ayyuka da dama, saboda haka ta kasance nasarar da aka samu bayan kokari da bangarori daban daban suka yi tare. Baya ga haka Ban ya bayyana imanin cewa, yarjejeniyar za ta sanya nuna fahimtar juna da hadin kai kan wasu matsalolin tsaron da ake fama da su a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama a cikin jawabinsa ya nuna yabo kan muhimmancin cimma wannan yarjejeniya a tsakanin kasar Iran da kasashen nan shida da batun nukiliyar Iran din ya shafa, kana ya bayyana cewa, an katse dukkan hanyoyin samun makaman nukiliya na Iran, ta yadda za a tabbatar da tsaron duniya.
Idan har Iran ta martaba wannan yarjejeniya, ana fatan dage mata takunumin da kasashen yammaci suka kakkaba mata a fannoni daban daban na tsawon shekaru.
Masu sharhi na ganin cewa, hanya guda ta warware duk wata irin takaddama game da makaman nukiliya, ita ce nuna adalci ga dukkan kasashe. (Ibrahim/Sanusi Chen)