150721-ya-kamata-kasashen-afrika-su-koyi-sin-bako.m4a
|
Kelley Sams, wata yar Amurka, ta ziyarci Nijer daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2000, don gudanar da aikin sa kai a wajen, inda ta koyi harshen hausa, kuma tana jin dadin zaman tare da mutane.
Daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2004, ta sake zuwa Nijer da Nijeriya, don taimaka wa likitocin ceton mutane.
Daga shekarar 2014, ta fara aikin koyarwa a jami'ar Marseille ta kasar Faransa, inda take nazarin harkokin kiwon lafiya a Afrika, a shekarar 2015, ta zo kasar Sin, don nazarin dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen Sin da Afrika a fannin kiwon lafiya, tana ganin cewa, sabo da kasar Sin ba ta taba mulkin mallakar kasashen Afrika ba, shi ya sa, ana gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata.
Bayan da ta ziyarci kasar Sin, ta gane ma idanunta ci gaban da Sin ta samu, tana fatan kasashen Afrika su ma za su samu irin babban ci gaba da Sin ta samu.(Bako)