150714-akwai-babbar-dama-wajen-yin-magunguna-bako.m4a
|
Ta ci gaba da cewa, kasashe 7 cikinsu har da Kamaru, Czech, Nijeriya, Falesdiu, Sri Lanka da Tanzaniya sun tura wakilai don halartar taron, kuma tana gani, taron yana da amfani sosai, da ma, a kasar Nijeriya, akwai irin zance cewa, abinci da magungunan da aka yi a kasar Sin ba su da inganci, amma bayan da ta zo, ta gane da idanunta game da shirye-shiryen yin rajista, da yadda aka yi abinci da magunguna a masana'antu, ta gano cewa, ana tabbatar da ingancinsu. Haka kuma tana fatan karfafa zukatan jama'ar Nijeriya da su kara amfani da magunguna da abinci na kasar Sin.
Haka kuma, Madam Momotu ta ce, nan gaba, ya kamata kasashen Sin da Nijeriya su inganta hadin gwiwa tsakaninsu, don kawar da wadannan jita-jita. Alal misali, ya kamata gwamnatin Sin ta tura wakilai zuwa kasar Nijeriya, don shirya taron fadakar da jama'a game da yadda aka yi magunguna da abinci a kasar Sin.
Ban da wannan kuma, Momotu ta ce, ba ma kawai, kasar Sin ta dauki mataki don daukaka ingancin magunguna da abinci ba, a cikin 'yan shekarun nan, kasar Nijeriya ita ma, ta tashi tsaye don sa ido game da wadannan fannoni, inda ta ce, "Kwanan baya, hukumar NAFDAC ta fidda sabon shirin cewa, dole ne kamfanoni masu yin magunguna su zama mambobin kungiyar masana'antun yin magungunan Nijeriya wato PMGMAN da mambobin kungiyar shigar da magunguna daga kasashen waje ta Nijeriya APIN, ke nan ya kamata su samu izini daga wajensu, kuma wannan zai yi amfani da kasar Nijeriya da ta sa ido game da wadannan fannoni."
Game da fannonin ci gaba da hadin gwiwar tsakanin bangarorin biyu, Madam Momoto ta ce, Nijeriya tana da yawan al'umma a duniya, kuma akwai babbar kasuwanni a kasar, yayin da a ko wace shekara, Sin ta kan yin magunguna da dama, nan gaba, ya kamata Sin ta kara sayar da wadannan magunguna ga kasar Nijeriya, kuma Nijeriya za ta koyi hanyoyin yin magunguna da rigakafi, da kyautata tsarin kiwon lafiya na kasar, kuma wannan hadin gwiwa zai kawo moriyar juna.(Bako)