150715-Takaddamar-Girka-da-EU-kan-bashin-da-ake-bin-kasar-Sanusi.m4a
|
Wannan mataki na Girka ya tilastawa kungiyar EU kiran taron gaggawa kan yadda za a warware wannan matsala. Inda shugaban hukumar kungiyar EU Jean-Claude Junker ya ce, muddin aka gaza daddale yarjejeniya game da bashin da ake bin kasar ta Girka, hakika kamfanonin Girka na iya durkushewa sannan tsarin bankunan kasar shi ma zai ruguje. Kazalika jama'ar kasar za su fada cikin wahala. Daga karshe kuma matakin na iya mummunan tasiri ga nahiyar Turai baki daya.
Wannan hali ya sanya kungiyar EU ta shirya tsaf ko da kasar Girka za ta fice daga cikin rukunin kasashe masu amfani da kudin Euro. Matakin da kungiyar ta EU ba ta fatan faruwarsa.
Masana na ganin cewa, wannan matsala ba kawai a Girka ko nahiyar Turai kadai za ta tsaya ba, da alamun za ta iya shafar sauran sassan duniya. Kuma wannan wani sako ne ga kasashen duniya cewa, duk wata irin hadaka ba za ta magance musu matsalar da suke fama da ita ba.
Don haka wajibi ne kowace kasa ta kasance mai dogaro da kanta a ko wane lokaci don gudun faruwar matsalar da ta afkawa Girka ba zato ba tsammani. (Ibrahim/Sanusi Chen)