in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu wani kayyadadden wa'adi da aka sanya game da kammala shawarwarin nukiliyar Iran, in ji bangaren Iran
2015-07-09 13:47:03 cri

Kamar dai yadda masu bibiyar kafafen watsa labaru suka sani, an cimma matsaya ta sake jinkirta wa'adin shawarwari game da batun nukiliyar kasar Iran, karewar wa'adin ne kuma a ranar 7 ga wata, matakin da ke nuna matsayin bangarori daban daban da abin ya shafa na rashin yin watsi da shawarwarin.

Tsakanin bangarorin, kasar Iran na kan gaba wajen amincewa da ra'ayin ci gaban shawarwarin, bisa aniyar soke takunkumin da aka sanya mata tun da dadewa.

Mista Abbas Araqchi, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran daya ne daga manyan mambobi a tawagar masu gudanar da shawarwari kan batun nukiliyar kasar sa.

Bayan da aka sake dage wa'adin shawarwarin, Mr. Araqchi da ke halartar shawarwari a Vienna ya zanta da kafofin watsa labaru, inda yake ganin cewa, batun jinkirta wa'adin shawarwarin bai haifar da wani babban tasiri ga Iran ba, duba da cewa Iran din ta shirya sosai kuma a kan lokaci.

Ya ce,

"Game da batun jinkirta wa'adin shawarwari kan batun nukiliyar Iran, kamar yadda na fada a baya, babu wani kayyadadden wa'adi da muka sanya game da kammala batun, sai dai muna fatan a cimma yarjejeniyar da za ta biya bukatun mu. Mun riga mun shirya sosai game da tsayawa a Vienna, har zuwa lokacin da za a kammala wannan aiki. Ko da yake ana ta kara jinkirta wa'adin, amma muna ganin cewa, shawarwarin na kusan karewa. "

Yayin da ake shawarwari kan batun nukiliyar Iran, kullum bangarori daban daban wadanda abin ya shafa na boye bakunansu, ba su son fayyace komai dalla dalla.

Amma game da aikin tsara yarjejeniya, Mr. Araqchi ya gaya wa manema labaru cewa,

"mataimakan ministocin harkokin wajen kasashen da suke halartar shawarwarin ne za su kula da aikin tsara abubuwan da za a tanada cikin yarjejeniyar, kuma ministocin za su tsaida kuduri kan wasu daga cikinsu. Idan sun samu sakamako kan wani batu, za mu fara shawarwari a kansa, sannan nan za mu rubuta shi cikin yarjejeniyar karshe idan mun samu daidaito kansa. Kawo yanzu dai an riga an tabbatar da yawancin abubuwan da za a tanada cikin yarjejeniyar. "

A ganin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov, har yanza ba a cimma daidaito kan matsaloli 7 ko 8 a cikin shawarwarin ba. Amma ra'ayin bainal jama'a na kasa da kasa sun yi hasashen cewa, tsarin soke takunkumin da aka sanyawa Iran, da batun binciken kayayyakin sojan Iran matsaloli biyu ne da suka rage. Game da batun, Mr. Araqchi ya bayyana cewa,

"Yanzu yawan manyan sabanin ra'ayi dake akwai bai wuce uku ba, amma akwai wasu kananan sabanin ra'ayi guda 7 ko 8, wadanda ministocin harkokin wajen kasa da kasa za su tattauna a kai. Game da raguwar yawan matsaloli, da matukar muhimmancinsu ga bangarori daban daban, ana fatan ci gaba da tattaunawa domin neman samun wata hanyar warware su, wadda da za ta iya samun amincewa daga bangarori daban daban."

Yanzu Iran na da takunkumin sayen makamai daga MDD, soke takunkumin ya zama daya daga cikin sharuddan cimma yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran, wanda kuma wata babbar matsala ce da ke fuskantar shawarwarin.

Mr. Araqchi ya bayyana matsayin Iran kan hakan, inda ya ce,

"kwamitin sulhu na MDD ya sanyawa Iran takunkumin sayen makamai, amma mun nuna bukatar ajiye batun a gefe guda yayin da muke tattauna, domin cimma yarjejeniyar warware batun nukiliyar kasar. Lallai ya kamata kasashen da ke yammacin duniya su daina mai da hankali kan batun sanyawa Iran takunkumi. Kasancewar yarjejeniya da takunkumi a sa'i daya ba abu ne da ya dace ba."

Ana daukar shawarari kan batun nukiliyar Iran a wannan karo a matsayin karo na karshe ne kan batun. Iran ta lashi takobin cimma yarjejeniyar, yayin da kasashen da ke yammacin duniya su ma ba su da shirin komawa gida gabanin cimma daidaito. Yanzu dai babu abin da ya rage illa a zuba ido a ga yadda za ta kaya, game da ci gaban batun da za a samu a cikin 'yan kwanaki masu zuwa. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China