in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin waje ta Sin ta yi suka kan rahoton da Amurka ta fitar dangane da harkokin soja
2015-07-03 21:16:11 cri
Kasar Sin ta bayyana takaici da rashin amincewa game da wasu abubuwan da ke tanada a cikin sabon rahoto kan manyan tsare-tsare a fannin soji da Amurka ta fidda tare da barazanar da tace ta ke fuskanta daga kasar Sin.

A game da hakan Sin tace ya zama dole Amurka ta dakile tunanin yakin cacar baka, ta bi daidaito da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, don ci gaba da kokarta wajen kafa sabon nau'in dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Madam Hua Chunying ta bayyana hakan a yau Jumma'a 3 ga wata lokacin da take amsa tambayoyin manema labaru game da wannan sabon rahoto kan manyan tsare-tsare a fannin soji na kasar da Amurka ta fidda.

Madam Hua ta ce, a kwanan baya, sojojin Amurka sun fidda rahoto kan manyan tsare-tsaren soji na kasar na shekarar 2015, inda aka nuna cewa, Amurka za ta ci gaba da inganta hakikanin hadin gwiwa game da harkokin soji da kasar Sin, amma a dayan hannu, ta ce, aikin gine-gine da Sin ta yi a tsibiran kudancin teku na kasar ya kawo halin kunci a yankin Asiya da tekun Fasific.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China