150708-Muhimmancin-shirin-ziri-daya-da-hanya-daya-ga-kasashen-duniya-Sanusi.m4a
|
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya tallata shirin a watan Satumba na shekarar 2013 a lokacin da ya kai ziyara kasar Kazakhstan. Sannan a watan Oktoban shekarar 2013 kuma ya fara gabatar da shirin hanyar Siliki ta ruwa a jawabin da ya gabatar a majalisar dokokin kasar Indonesia.
Shi dai wannan ziri (Belt) ya kunshi kasashe ne da ke kan hanyar siliki, kuma ya ratsa zuwa tsakiya da kuma yammacin Asayi, gabas ta tsakiya da kuma Turai. Da farko shirin na kira ne a hada kai wajen samar da kayayyakin more rayuwa, kara musayar al'adu, fadada cinikayya da sauransu.
Bayan wannan ziri na siliki, daga bisani sai aka fadada shi zuwa kudanci da kudu maso gabashin Asiya, kuma galibinsu mambobin bankin zuba jari na Asiya ne wato AIIB.
Masana na ganin cewa, wannan tunani ko shiri zai kara baiwa Sin damar taka muhimmaiyar rawa a harkokin kasa da kasa da bukatarta ta fitar da kayayyakin da take kerawa zuwa ketare, kamar na'urori da sauran muhimman kayayyakin zamani da kasuwannin duniya ke bukata a halin yanzu.
Bugu da kari, shirin zai mai da tsoffin hanyoyin da fatake ke amfani da su a zamanin da wajen gudanar da harkokinsu na saye da sayarwa har ma suka fadada zuwa auratayya, musayar al'adu, fasahohi, sada zumunta da sauran muhimman fannoni na rayuwa. (Ibrahim/Sanusi Chen)