150701-Takaddamar-kotun-ICC-da-shugabannin-Afirka-Sanusi.m4a
|
A wata sanarwar da kotun ICC din ta fitar ta ce, har yanzu takardar sammacin neman damke shugaban na Sudan da ke ziyarar aiki a kasar da kotun ta bayar na nan daram kuma kasancewarta mambar kotun ta ICC, Afirka ta kudu na da hakkin da ya rataya a wuyanta na tsare shugaba Al-Bashir da zarar ya sauka a cikin kasar.
Sai dai duk da wannan umarni da kotun ta ICC din ta aike, a baya ma kungiyar AU ta ki baiwa kotun hadin kai inda ta zarge ta da yi wa shugabannin kasashen Afirka bita-da-kulli.
Masu sharhi na kallon matakin kotun a matsayin nuna son kai ko karkata ga kama shugabannin Afirka kadai, inda suka ce kotun ta bar jaki ne tana dukan teki.
Kotun ICC ta ce, tana tuhumar shugaba Al-Bashir ne da zargin aikata laifuffukan yaki da na keta hakkin bil-Adam a yankin Darfur da sauran sassan kasar, zargin da mahukuntan Sudan din suka karyata.
Ko a baya ma, sai da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya gurfana gaban kotun ta ICC bisa zargin aikata wasu laifuffuka, zargin da shi ma ya gamu da fushin shugabannin na Afirka kafin daga bisani kotun ta wanke shi. (Ibrahim/Sanusi Chen)