in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi tir da hari kan tawagar MDD a Mali
2015-07-03 09:48:15 cri

Kwamitin tsaron MDD ya yi matukar Allah wadai da harin ta'addanci da aka kaiwa tawagar MINUSMA, mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali, lamarin da ya sabbaba rasuwar jami'an tawagar 6, tare da raunata wasu mutane 5.

Da sanyin safiyar jiya Alhamis ne dai wasu mahara suka yiwa tawagar kwantan-bauna, a kusa da birnin Timbuktu dake yankin arewacin kasar mai yawan fama da tashe-tashen hankula.

Wata sanarwa da aka rabawa manema labaru ta bayyana cewa, jami'an da aka hallaka yayin harin 'yan asalin kasar Burkina Faso ne. kuma kawo yanzu ba a kai ga tantance ko su waye maharan ba.

Tuni dai kwamitin tsaron ya umarci gwamnatin Mali da ta gaggauta gudanar da bincike, domin gano, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta'asa gaban kuliya.

A wani ci gaban kuma, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi tir da aukuwar wannan hari, yana mai gargadi ga daukacin masu kaiwa jami'an MDD hare-hare da su san cewa, laifin da suke aikatawa ya yi matukar keta dokokin kasa da kasa.

Cikin wata sanarwa da mataimakin kakakin sa Farhan Haq ya fitar, Mr. Ban ya bukaci da a gaggauta gurfanar da wadanda suka aikata wannan mummunan laifi gaban kuliya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China