150701-ba-za-mu-manta-da-karatunmu-a-Sin-ba.m4a
|
Daga ranar 21 ga watan Mayu, kwararru da jami'an a fannin noma kimanin 32 da suka fito daga kasashe masu tasowa 12 sun zo kasar Sin don halartar wani taron kara-wa-juna-sani game da aikin gona, inda Malam Farouk da Malam Kabiru da Malam Lawal da suka fito daga jihohin Katsina da Sokoto na tarayyar Nijeriya, sun bayyana cewa, ba za su manta da zamansu a kasar Sin ba, sabo da karatun da suka samu da abokansu daga kasashen daban daban.(Bako)