in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD na fatan za a cimma yarjejeniya a shawarwarin da za a gudanar da 'yan tawayen Mali
2015-06-19 09:54:33 cri

Kwamitin tsaron MDD ya bayyana fatan kaiwa ga cimma yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya, yayin shawarwarin da wakilan gwamnati, da na gamayyar 'yan tawayen kasar Mali za su gudanar a gobe Asabar.

Wata sanarwa da wakilan kwamitin tsaron suka fitar, ta ja hankalin daukacin sassan masu ruwa da tsaki a kasar ta Mali, da su kaucewa daukar dukkanin wani mataki da ka iya gurgunta shawarwarin da za a fara. Su kuma sanya burin wanzar da zaman lafiya a kasar gaban komai.

A ranar 15 ga watan Mayun da ya shude, tsagin gwamnatin kasar ta Mali ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya, da wasu kungiyoyin 'yan tawayen kasa 3, ko da yake gungun kungiyoyin 'yan tawaye wadanda kungiyar Azbina ta CMA ke jagoranta, ba su shiga tattaunawar ta wancan lokaci ba. Sai dai a wannan karo, ana sa ran CMAn za ta shiga tattaunawar.

A baya dai CMA ta taba bayyana aniyarta, ta rattaba hannu kan yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da tsagin gwamnatin kasar ta Mali, ta kuma sanya hannu kan wata kwarya-kwaryar yarjejeniya da mahukuntan kasar a ranar 14 ga watan Mayu, ko da yake ta ce akwai wasu sassa na yarjejeniyar, da ya zama wajibi a tattauna su, tsakaninta da masu shiga tsakani da kuma gwamnatin Malin.

Dubban al'ummar kasar Mali ne suka gudanar da wani jerin gwano a ranar 27 ga watan Mayun da ya shude a birnin Bamako, a wani mataki na nuna goyon baya ga yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya tsakanin sassan biyu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China