in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin yankin Hongkong ta ki zartas da shirin gyara hanyar zaben kantoma
2015-06-18 13:50:02 cri

A yau ne majalisar dokokin yankin Hongkong na kasar Sin ta yi watsi da kudurin da aka gabatar mata na yin gyara kan tsarin da ake bi wajen zabar kantoman yankin. A wannan rana da karfe 12 da minti 35 ne, aka kammala jefa kuri'u kan wannan kuduri, a sakamakon haka, shirin gyara game da zaben kantoman yankin bai samu kashi 2 cikin 3 ba na kuri'un da ake bukata kafin shirin ya samu nasara.

Gwamnatin yankin musamman Hongkong ta kira taron tattaunawa game da gyara dokar zaben kantoman yankin. Bayan sa'o'i 9 da aka kwashe ana tabka muhawara, 'yan majalisu 41 daga cikin 70 sun yi jawabi, daga bisani, an kawo karshen muhawarar da karfe 12 na ranar yau, sannan aka fara jefa kuri'u kan shirin da karfe 12 da rabi.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China