150605-ranar-kiyaye-muhallin-duniya-lubabatu.m4a
|
Ranar 5 ga watan Yuni na kowace shekara rana ce da MDD ta kebe musamman domin kiyaye muhalli. Idan an waiwayi baya, daga ranar 5 zuwa ranar 16 ga watan Yunin shekarar 1972, MDD ta kira wani taro a birnin Stockholm, babban birnin kasar Sweden, inda aka tattauna batun kiyaye muhallin duniya, taron da ya zama na farko a tarihin dan Adam aka yi nazari a kan harkar kiyaye muhalli a fadin duniya. A gun taron, an yi kiran cewa, duniya daya kacal gare mu. Daga baya, a watan Oktoba na waccan shekara, babban taron MDD karo na 27 ya kebe ranar 5 ga watan Yuni na kowace shekara a matsayin ranar kiyaye muhallin duniya, a yunkurin jawo hankalin al'ummar duniya a kan muhallinsu da kuma barnar da suke kawo wa muhalli, domin bayyana musu muhimmancin kiyaye muhalli. To, shin wadanne matsaloli ne ake fuskanta ta fuskar kiyaye muhalli a nan kasar Sin? Wadanne matakai ne aka dauka? Sai a biyo mu cikin shirin, Domin samun karin haske.(Lubabatu)