150617-An-kafa-dokar-hana-shan-Taba-sigari-a-bainar-jamaa-a-birnin-Beijing-Sanusi.m4a
|
Masana na ganin cewa, sabuwar dokar da mahukuntan birnin Beijing suka bullo da ita, za ta taimaka wajen hana zukar Taba-sigari a wuraren da jama'a ke taruwa a sassan birnin, Wannan ya sa jami'an hukumar lafiya ta duniya WHO ke cewa, kasar Sin ta cika alkawarin da ta yi na dakile shan Taba-sigari a bainar jama'a.
Jami'an hukumar lafiya ta duniya sun bayyana cewa, wannan mataki da mahukuntan birnin Beijing suka dauka ya haifar da kyakkyawan sakamako a wannan fanni da kuma yarjejeniyar yaki da shan Taba-sigari da aka cimma da hukumar ta WHO.
Alkaluma na nuna cewa, sama da mutane biliyan 1.1 ne ke busa taba-sigari a sassa dabam-daban na duniyar nan, dabi'ar da masana harkar lafiya a kullum ke gargadin jama'a da su nisance ta sakamakon illar ta ga koshin lafiyarsu.
Sai dai yayin da wasu rukunin jama'a ke maraba da wannan mataki, su kuwa masu samar da tabar na kukan irin asarar da za su tabka da kuma raguwar irin makuden kudaden da suke samu daga wannan sana'a, inda kididdiga ke nuna cewa, kashi 10 cikin 100 na kudaden shigar da gwamnatin ke samu na zuwa ne daga bangaren taba-sigari.
Abin jira a gani shi ne, ko wannan doka za ta yi tasiri ko kuma a'a. (Ibrahim/Sanusi Chen)