150610-Matakan-sabon-shugaban-Najeriya-na-dawo-da-matarbar-kasar-Sanusi.m4a
|
A jawabinsa na bikin rantsuwar kama aiki wanda ya samu halartar shugabannin wasu kasashen duniya ko wakilansu, jami'an diplomasiya da sauran manyan baki da ya gudana a dandalin Eagle da ke Abuja, babban birnin kasar Najeriya, shugaba Buhari ya jaddada alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabe, wato yaki da cin hanci da rashawa da batun tsaro, samarwa matasa aikin yi, matsalar hasken wutar lantarki da sauransu.
Masu sharhi sun bayyana cewa, jawabin shugaban na Najeriya ya sake tabbatar da matsayinsa na mutum mai son nuna gaskiya da aiki ba sani ba sabo don ceto kasar daga mummunan halin da ta fada.
A kokarin da yake na tabbatar da maganarsa game da yaki da kungiyar nan ta Boko Haram, shugaban ya fara rangadinsa na farko tun bayan rantsar da shi zuwa kasashen Nijar da Chadi da kuma Kamaru don neman goyon bayansu a yakin da ake da mayakan na Boko Haram.
Wannan ne karo na farko a tarihin Najeriya da jam'iyyar adawa ta kwace mulki a hannun jam'iyya mai mulki.
Ana dai yi wa sabuwar gwamnatin zaton aikata ayyukan alheri, sai dai akwai bukatar 'yan Najreriya da su ma su kasance masu bin doka da oda don ba da tasu gudummawa a kokarin da sabuwar gwamnatin ke yi na maido da martabar kasar a idon duniya daga dukkan fannoni. (Ibrahim/Sanusi Chen)