in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana tantance asalin wadanda suka rasu sakamakon nutsewar jirgin ruwan fasinja a kogin Yangtze
2015-06-07 13:14:00 cri

Babban daraktan hukumar kula da harkokin zamantakewar al'umma, a ma'aikatar harkokin jama'a ta kasar Sin Zhang Shifeng, ya ce yanzu haka ana gudanar da aikin tantance asalin fasinjojin da suka rasu, sakamakon nutsewar da jirgin ruwan dake dauke da su ya yi a kogin Yangtze. Mr. Zhang ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru karo na 13 da aka shirya a Asabar din nan, game da batun nutsewar jirgin na "Dongfangzhixing". Zhang ya kara da cewa an kusa kaiwa ga karshen wannan lamari, duba da cewa a yanzu haka muhimmin aikin da aka sanya gaba shi ne jana'izzar wadanda hadarin ya ritsa da su, domin kwantar da hankalin iyalansu. Bisa al'adar Sinawa, kwanaki 7 da rasuwar fasinjojin dake cikin jirgin ya dace a gudanar da bikin tunawa da su. Don haka ma'aikatar sufuri ta kasar Sin, ta shirya biki ta hanyar busa kakaki daga wasu manyan jiragen ruwa, tare da baiwa ma'aikatan jiragen damar gudanar da zaman makoki a kusa da wurin da jirgin ruwan ya nutse, domin nuna alhinin wadanda suka rasu. Ya zuwa karfe 11 na ranar Lahadi din nan, yawan mutanen da suka mutu sakamakon wannan hadari sun kai mutum 431, kana akwai sauran mutane 11 da ba a san a ina suke ba tukuna. Kaza lika hukumomin sufurin kasar Sin sun kebe jiragen ruwa 254, da ma'aikata 2504, domin ci gaba da neman sauran mutanen. (Sanusi Chen)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China