150601-Mai-da-hankali-kan-batun-marayu-Bilkisu.m4a
|
Yanzu ana ta kara mayar da hankali kan batun yara, aboda su ne makomar kasa, kuma fata ne na al'umma. Kamata ya yi a samar masu da yanayi mai kyau a fannonin iyalai, al'umma da kuma karatu, domin su iya yin girma cikin alheri tare da kiwon lafiya da kuma farin ciki.
Wannan ne burin da kasashe daban daban suke kokarin cimmawa. Amma, yanzu akwai wasu yara na musamman wadanda suka rasa Iyayen wato suka zama marayu bisa wasu dalilai, ko su iyayensu suka mutu, wassu Yaran kuma Iyayen na da rai amma dalilin an haise su da nakasa ko wani mummunar rashin lafiya, Iyayen sun yar da su suna ji suna gani saboda ba su da karfin ba su jinya. A cikin wannan rana ta musamman ta yara, a gani na kamata ya yi mu ma sa yi nazarin kan irin wadannan yara bayin Allah masu baiwa na musamman.
A kwanan baya wakilinmu dake Nigeriya Murtala ya kai ziyara ga wani gidan marayu a birnin Kano a Arewacin Najeriya, don ganin yadda wadannan yara na musamman suke. A nasu bangaren ma Bilkisu da Kande ma sun tafi birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin, don ziyarar wani gidan marayu nakasassun.