Bisa bayanin da jaridar Ghanaian Times ta bayar a jiya Alhamis 28 ga wata, an ce, Amissah-Arthur ya yi wannan furuci ne ranar Laraba a birnin Accra babban birnin kasar, yayin da yake ganawa da wata tawagar Sin dake karkashin shugabancin Zhou Yuxiao, manzon musamman dake kula da harkokin dandalin tattaunawar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika
Mr. Kwesi ya yi kira ga masana'antu masu zaman kansu na Sin da su yi amfani da kyakkyawan yanayin da Ghana ke ciki a yanzu don saka jari a kasar, kuma yana sa ran hukumar hada-hadar kudi ta Sin za ta bude rassansu a kasar don kara taimakawa 'yan kasar Ghana da ke kasuwanci a kasar Sin.
Kazalika kuma, ya yabawa gwamnatin Sin bisa rancen da ta bayar don gudanar da manyan ayyukan a kasar, kamar masana'antar sarrafa iskar gas ta Atuabo, da hanyoyin mota da layin dogo da sauran muhimman ababen more rayuwa.
A nasa bangare, Mr. Zhou ya ce, Sin ta kebe kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 500 don raya muhimman ababen more rayuwa a kasashen waje, don haka ya kuma bukaci Ghana da ta yi amfani da wannan dama.
Ya ce, Sin na kokarin canja salon bunkasuwar dangantakar cinikayya dake tsakaninta da tsoffin abokanta, musamman ma ta fuskar raya masana'antu da sauransu, kuma Sin na son taimakawa kasashen Afrika da fasahohinta ba tare da wata rufa-rufa ba.(Bako)