150527-Makomar-yan-gudun-hijirar-Rohingya-Sanusi.m4a
|
Sai dai bayan da kasashen Malaysia, Thailand da Indonesia suka amsa kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi musu kan su yi wa Allah su baiwa wadannan 'yan gudun hijira galibinsu yara, mata da kuma tsoffi da suka galabaita kusan dubu 7,000 mafaka na wucin gida kafin a lalubo bakin zaren warware wannan matsala.
Kasashen Malaysia da Indonesia ne suka fara amincewa da wannan bukata ta baiwa 'yan gudun hijirar da suka galabaita sakamakon kwashe kwanaki a kan teku ba tare da samun abinci da ruwan sha da kuma sanin inda suka dosa ba mafaka.
Yanzu dai wadannan kasashe sun yi alkawarin baiwa wadannan 'yan gudun hijirar Rohingya matsuguni na wucin gadi wato shekara guda kafin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD da sauran hukumomin da abin ya shafa su samar musu matsuguni na din-din-din.
Masu sharhi na ganin cewa, kamata ya yi a samo mafita ga wannan matsala ta 'yan ci-rani da ke ci gaba da zama babbar damuwa ga duniya a wannan lokaci.
Bugu da kari masana na cewa, muddin ba a kawar da nuna duk wani bambanci kamar na addini, kabilanci ko yare ba, batun matsalar 'yan ci-rani ba, na iya zama abin da malam Bahaushe ke cewa, Kaikayi. (Ibrahim/Sanusi Chen)