150526-Nijeriya-za-ta-ci-gaba-da-tabbatar-da-kwagilolin-dake-daddale-da-Sin-bako.m4a
|
Kwanan baya, yayin da babban jami'in zartaswa na hukumar kula da harkokin kimiyya da gine-gine (National Agency for Science&Engineering Infrastructure) na Nijeriya Engr.Dr. Mohammed Sani Haruna ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka kafa hukumarsa shi ne, don raya harkokin kimiyya da fasaha da masana'antu. Yanzu, bayan da shekaru 22 da suka wuce, Nijeriya ta yi hadin gwiwa da wasu kasashen duniya, ba ta samu ci gaba sosai kam.
Yanzu, bayan da Nijeriya ta kara karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannin masana'antu da kimiyya da fasaha, Sin ba ta boye-boye, kuma ta hanyar hadin gwiwa da Sin, Nijeriya ta koyi wasu abubuwa daga cikinsu. Alhaji Haruna ya ce, ya zo Sin ne don gaya wa Sinawa, za a ci gaba da hada hannu dake tsakanin Nijeriya da Sin, ba wai za a dakile hadin gwiwa don canjin gwamnati ba.
Ya ce, bisa dokokin Nijeriya, duk shugaban Nijeriya, zai zama shugaban hukumar NASEI, a matsayinsa babban mashawarcin sabon shugaban Nijeriya a fannin kimiyya da fasaha da masana'antu, zai gaya masa abubuwan da ya ganema idanunsa a kasar Sin, tare da ba shi shawara cewa, ya kamata a hada fasahohin da Sin ta samu da 'yan kwadago da albarkatun da Nijeriya take da shi. Sannan kuma, a raya hadin gwiwa dake tsakanin kananan 'yan kasuwa dake tsakanin bangarorin biyu da sauransu.(Bako)